Spread the love

Gwamnatin Zamfara Ta Kaddamar Da Kwamitin Dazai Bada Shawara Kan Yansandan Jama’a

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammed Matawalle, Ya Kaddamar da wani kwamiti da za ya ba da shawara akan yanda za’a tantance ‘Yan sandan jama’a.

Waɗan da aka Kaddamar sun hada kwamishinan ‘Yan sandan jihar, CP Usman Nagogo, a matsayin shugaba na daya, da maimartaba sarkin Zamfaran Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad CON, a matsayin shugaba na biyu.

Membobin kwamitin su ne, Birigediya O M Bello, Daraktan ‘Yan sandan farin kaya, Daraktan hukumar tsaro ta civil defence, da wakilan addinai da dai sauran su.

Da yake jawabi Jim kadan bayan Kaddamar da wannan kwamitin, a garin Gusau babban birnin jihar, Gwamna Matawalle yace, ya Kaddamar da su ne domin a gaggauta samar da shawara mai ma’ana ta yadda za’a samu mutane na gari wajen wannan aikin, domin magance matsalar tsaron da wannan jihar ke fuskanta.

Daga nan ya gargadi yan kwamitin dasu dage damtse, domin gudanar da jan aikin dake gaban su, kuma ya shawarce su da su yi la’akari da dokokin kasa wajen aikin nasu.

” Idan muka samu Yansandan Jama’a, to zamu ji saukin samun bayanai sahihai game da abinda ke faruwa a duk fadin jihar nan, kuma za su yi aiki kafada da kafada da ‘Yansandan mu, domin kaucewa rudani’. Inji Gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *