Spread the love

Atiku ya ba da shawarar taimakon mabuƙata kafin sanya musu dokar zama a gida


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjinawa gwamnatocin jihohi kan matakan da suke dauka irinsu sanya dokar zama a gida, rufe wasu kasuwanni, da wasu wuraren da ake taruwa sosai da fitar da tsarin hulɗa a cikin mutane.


Ya ce dole ne sai an fahimci dayawan mutane suna da matsalar kuɗi don amfani da su in sun keɓe kansu a gida, da haka yakamata gwamnati mai ci ta tarayya ta ɗauki matakan samar da abubuwan da za su taimaki mutane su rayu in dai har ana son su yi biyayya ga matakan kare kai da aka sanya musu.


Yana ganin mutane miliyan 30 in kowanensu ya samu dubu 10 don ya sayi kayan abinci ba wanda zai ga an barshi baya.


Yayi kira ga kamfunan layin waya su baiwa mutum miliyan 100 kyautar kuɗin kiran waya a ƙalla su ba su naira 1500 ga kowane layi domin duk wanda ya ga alamun ciyon gare sa sai ya kira Su duba a duba a ɗauki mataki.

Shi a ƙashin kansa ya ba da miliyan 50 a asusun da za a tara kudin da za a taimakawa al’umma don saukaka musu kan wannan annobar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *