Spread the love

Masu Garkuwa da Mutane Sun Sako Uban Kasar Wuya, tare da dansa da Mutane 13

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A yau Talata ne Gwamnan Jihar Zamfara  Bello Muhammed Matawalle ya karbi Uban Kasar Wuya, Alhaji Umar tare da dansa malan Maniru da wasu Mutane goma sha ukku, da ‘yan bindiga suka sako, bayn garkuwa da su.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar bayani, wadda mai baiwa Gwamna shawara  na musamman a  fannin yada labarai, da wayar da kan jama’a Alhaji Zailani Bappa ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai,  a garin Gusau babban birnin jihar.

 Da yake jawabi lokacin  karbar mutanen, a hannun Kwamishinan yansanda Alhaji Usman Nagogo, Gwamna Matawalle yasha alwashin kakkabe yan ta’addan da suka ki yadda da sulhu, da kuma duk wani mai taimaka masu.

 “Gwamnatin mu ta canja matakan sulhu, inda zamu ci gaba da fatattakar wanda duk ya bijire wa wannan shirin namu na zama lafiya, domin jami’an tsaron mu za su kama da kuma gurfanar da duk wanda aka kama gaban kuliya manta sabo”.

“Mun rigaya mun shirya duk abinda ya kamata tsakanin mu da sojoji, inda za mu yi aiki tukuru, mu yi farautar duk wanda yaki rungumar sulhun da aka yi, duk inda suke a fadin wannan jihar.” Matawalle ya ce.

 Gwamna Bello Muhammed Matawalle, ya kara da cewa yanzu haka an samu nasarar cafke mutun bakwai wadanda ake zargi da tsegun tawa ‘yan ta’addan labari, (informants). Kuma suna nan hannun hukuma, ba da dade waba za’a tusa keyarsu zuwa Abuja, hakama duk wanda aka kama yana taimaka wa ‘yan ta’adda wajen tsegun ta masu labarai to zai yabawa aya zaki.

Haka zalika, ya gargadi sarakunan gargajiya da cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa haramtacciyar kungiyar nan ta ‘Yan sa-kai, to ya sani bakin rawaninsa kenan, domin gwamnati ta haramta ayukkan yan sa-kai a Zamfara.

Daga karshe Gwamnan ya ba da umurnin duba lafiyarsu, kafin daga baya a hada su da ‘yan uwansu da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *