Spread the love

Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa  3 Sun Kamu Da Cutar Kurona  

    Rahoton da yake fito daga fadar shugaban kasa na nuna cewa ma’aikatan ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa  Abba Kyari, su  uku sun kamu da cutar Kurona (COVID-19) kamar yadda TheNation ta ruwaito.

 An yi yunkurin ji daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa amma ba a samu nasara ba saboda gaba daya ba a ga  Garba Shehu da Femi Adesina a fadar ba, wasu na zaton ko sun shiga buya ne.

 Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari su je domin duba lafiyarsu.  

Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma’aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba, kan harkar duba lafiyar ko fargaba.  

Bugu da kari, dukkan ma’aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ba su shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa.

 A yanzu dai, da alamun ana shirin kulle fadar shugaban kasar saboda an umurci dukkan dukkan ma’aikatan su koma gida, sai yanda hali ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *