Spread the love

Abba Kyari Ya Kamu Da Corona Virus, Atiku ya yi masa addu’ar samun sauƙi

Sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.

Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya ɗauke da ƙwayar cutar a safiyar yau a Abuja.

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.

Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami’an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi wa shugaban fadar gwamnati Abba Kyari addu’a da roƙon Allah ya bashi sauki ya kare sauran waɗanda ba su kamu ba.

Wannan addu’ar ya yi ta ne saman turakarsa ta facebook bayan fitar da bayanin Abba ya kamu da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *