Mai tsaron baya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya Shehu Abdullahi ya yi addu’ar samun sauki daga Allah kan ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Enyimba Dare Ojo wanda aka yi garkuwa da shi da ya kuɓuta da sauri.

Ɗan wasan mai take leda Bursaspor ta jihar Turkeƴ ya nuna matuƙar damuwarsa kan yanda matsalar tsaro ke waita a Nijeriya, ya yi kira ga gwamnati ta samar da kyakkyawan yanayi ga kowa.

Tsohon ɗan wasan Kano ƙwararren ɗan wasan tsakiya ya maganta kan abin da ke samun ‘yan wasan a Nijriya musamman abin da ya samu Ojo kan hanyarsa ta zuwa Akure ya nemi sauƙin Allah ya kuɓutar da shi.

A turakarsa ta twitter ya rubuta ya samu labarin abin ya faru da ‘yan wasan biyu a Nijeriya Ifeanyi George da ya haɗu da haɗarin mota ya rasa ransa da Ojo da aka yi garkuwa da shi dukansu ya yi masu addu’ar sauƙi daga Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *