Spread the love

Gwamnan Bauchi Ya Killace Kansa, Bayan Sun Gaisa da ɗan Atiku da ya kamu da Cutar Corona 

Wani makusancin Gwamanan Baichi Bala Muhammad,  Ladan Salihu ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa; Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya killace kan shi sakamakon gaisawa da ya yi da Aliyu Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar Corona, a lokacin da suka haɗu a cikin jirgin sama.


Ya ce “Tabbas sun gaisa da ɗan gidan Atiku kuma suna tare da shi a jirgin sama daga Lagos zuwa Abuja har ma sun ɗan yi hira, yanzu haka Gwamna da sauran mutane suna ɗakin gwaji kuma muna fatan ba su kamu ba” Inji Ladan Salihu.

Wannan annobar tana yaɗuwa a duniya kamar wutar daji yayin da a  Nijeriya lamarin ke faɗaɗa a yanzu an samu yanayin cutar ga wasu mutane 30 bayan kashe ɗaya daga cikin mutanen da ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *