Spread the love

Jam’iyar PDP da APC sun kaure da cacar baki kan hukuncin da ake jira na sake duba hukuncin kotun ƙoli kan zaɓen gwamnan Zamfara.

Sakataren yaɗa labarai na APC Malm Lanre a bayanin da ya fitar ya ce PDP ta fitar da bayanin cewa kotun ƙoli ba ta wani madogara face ta jefar da koken da aka shigar gabanta wannan tirsasa kotu ne.

Ya yi kira ga kotun ƙoli ta fusknci abin da yake gabanta ta yi adalci kalaman PDP ba su da kai balle makama.

Sakataren yaɗa labarai PDP Kola ya shawarci APC da su daina tunanin sake duba hukuncin kotun ƙoli zai goyi bayansu.

Ya yi kira da kotun ƙoli ta fita batun matsin APC kar ta duba hukuncin da ta gbatar da kanta.

Ya ce suna sane da irin shige da ficen da wasu magoya bayan APC ke yi ba dare ba rana domin a yi hukuncin da zai sanyaya musu rai ta bayan taga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *