Bashin miliyan 34: Tsohon shugaban ƙaramar hukuma ya yi Allah ya isa abin da ake kallo ƙarara da gwamnatin Tambuwal yake


Tsohon shugaban ƙaranar hukumar Sokoto ta Arewa Alhaji Abdullahi Hassan ya yi shaguɓe da ake zaton da gwamnatin Gwamna Aminu Waziri  Tambuwal yake kan bashin da yake bin gwamnati ba a biya shi ba.

Abdullahi a kan turakarsa ta facebook ya yi dogon rubutu kan kudinsa da matsayrsa, tare da bayyana jagoran gwamnati ya yi amai ya lashe kan cigaba da daukar nauyin karatun mata a matakin sikandare wanda a farko ya dakatar.


“Ka rike kudin makarantar ɗan jihar sokoto ₦34m Na Yara 73, na shekara 2 wadan da wasunsu na nan Jami’ar Sokoto Suna karatun likitanchi mataki na hudu (400L), ka yi doka ba ka sake daukar nauyi ‘yan sakadare, don kawai ka karya ta, yanzu kuma ka wal-wale” 


“Allah ba mutum ba ne kuma ya’isa, za ku ga sakamakon zalunci ba da daɗewa ba insha Allah.” in ji Abdullahi.
 

Ya ce har ya manta da wadannan kudade, Sai yanzu wani rubutu na ɗaukar yara 60 da za su makaratar Sikandare a garin Minna ta jihar Neja da garin Zariya na jihar Kaduna  ya tuna masa.


“Allah, ko da ba su Sanka ba, ka yi gaggawar isar min ga duk mai hannu ga wannan lamarin na ɓoye da bayyane, Allah ka Bani Ikon mantawa da su, Allah ka biyani ta wani wajen da ba su zato.” addu’ar Hassan kan bashin da yake biya.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *