Sanata Wamakko ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yawaita addu’ar samun mafita ga cutar Korona-baros

Sanata Wamakko ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yawaita addu’ar  samun mafita ga cutar Korona-baros

Daga Muhammad Muhammad

Annobar cutar Korona-baros  da ta addabi duniya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko mai wakiltar yankin Sokoto ta Arewa ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yawaita addu’ar samun mafita ga cutar  Korona-baros.

Sanata Wamakko ya yi wannan kiran ne a  ranar Jumu’a data gabata a gidansa dake unguwar Gawon Nama cikin birnin Sokoto a lokacin da yake yi wa magoya bayansa bayani jimkadan bayan dawowarsa daga Abuja.

Sanata Aliyu Wamakko ya ce annobar ba shakka daga Allah ne ba wani shakku a kai, kuma shi ne zai kawo mafita a cikin halin da ake ciki.

“In muka yawaita addu’a Allah zai tausaya mana Ya kawo muna karshen wannan annoba.”

Sanata ya yi kira ga mutanen Nijeriya su bi umarnin jami’an lafiya ga shawarwarin da suke bayarwa a matakin jiha da kasa, kamar wankin hannu da shan ruwa akai-akai.

Sanata Wamakko a takardar bayani da mataimaki na musamman kan yada labarai Bashir Rabe Mani ya sanyawa hannu ya yi kira ga jama’a su rika sauraren yekuwar wayar da kai kan cutar da ake yi a kafafen yada labarai.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *