Ko goyon bayan Ganduje ga Tinubu na iya sanya ya samu nasara a 2023?

Gwamnan Kano Dakta Umar Abdullahi Ganduje a kwanan nan yana ziyartar jigon jam’iyar APC Sanata Bola Tinubu abin da ake dangantawa da harkokin siyasar 2023.

Ƙarara ana hasashen Tinubu nada sha’awa da neman kujerar shugban ƙasa bayan shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa, sai dai har yanzu bai fito ya nuna aniyarsa ba, a halin yanzu a Arewa ba wani gwamna da ya fito ƙarara ya nuna hulɗarsa da Tinubu sama da Ganduje da ake ganin yana ziyartar jigon.

In har Tinubu zai yi takarar Ganduje da dukkan goyon bayansa na iya Sanya Tinubun ya samu kai bantensa a 2023 ganin yanda yake tattare da ƙalubale a siyasar jihar Kano, ga batun wa zai gaje shi, wace kujera zai nema bayan wa’adin gwamna ya cika, a gefe ɗaya magoya bayan Kwankwasiya na jiransa domin fafatawa da wanda ya tsayar.

Har yaushe ne Ganduje ya kammala waɗan nan ya koma waje ya taimaki ɗan takarar shugaban ƙasa a samun nasara hakan ne ake ganin yana da wuyar gaske Ganduje ya iya taka wata rawa da za ta iya kawo sauyi ga nasarar Tinubu.

Ko mine ne dai lokaci zai iya bayyana komi ko ƙawance zai nare ko lissafi zai canja a dai jira lokaci don shi ne alƙalin kowane hasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *