An shawarci jam’iyar PDP ta tsaida Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sunusi takarar shugaban ƙasa a 2023

An shawarci jam’iyar PDP ta tsaida Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sunusi takarar shugaban ƙasa a 2023


Dakta Umar Ardo wanda fitaccen dan siyasa ne kuma masani a Arewacin Nijeriya, ya yi hira da Jaridar Daily Trust inda ya tabo batun 2023 da kuma tsige Sarkin Kano da aka yi. 


A na sa ra’ayin Umar Ardo ya na ganin cewa gwamnatin APC ta buga kataɓora wajen tsige Muhammadu Sanusi II da kuma barka masarauta da Gwamnatin Kano ta yi a 2019. 


A siyasarsu ta PDP kuwa, Jagoran jam’iyyar ya na ganin cewa Muhammadu Sanusi II zai iya zama kadara ga jam’iyyar PDP, wanda ya ce tunɓukesa da aka yi zai iya zama masa alheri.


 Dakta Ardo ya bayyana cewa ya na da ra’ayin bai kamata a fara maganar takarar Muhammadu Sanusi II a yanzu ba, ya ce ya kamata ne a wannan lokaci tsohon Sarkin ya wartsake tukuna.


 “Ina son shi, kuma ina ganin cewa za ayi dacen shugaban kasa idan ya samu mulki. Idan har ya ji maganar mutane ya tsaya takara, zai ci zabe. Ina maso kallon cewa zai kai labari.” Inji sa. 


Sai dai idan har tsohon gwamnan babban bankin zai shiga siyasa, Ardo ya na ganin jam’iyyar PDP mai adawa ce ta fi dacewa da shi ba jam’iyyar APC ta Abokinsa Gwamna Nasir El-Rufai ba.


 “A wani ɓangaren, cire masa rawani ya na iya zama mafitar matsalolin shugabancin Arewa. Duk mun san cewa Arewa ta dade ta na neman shugaba, eh mun san ‘Dan Arewa ya ke mulki.”


 ‘Dan siyasar ya kara da cewa: “Amma gazawarsa na kawo karshen matsalolin kasar musamman na Yankin Arewa, game da tsarin shugabancinsa (Buhari) ya sa ‘Yan Arewa sun ji kunya.


 Ya ce: “Duk inda Sanusi II ya je, magana daya ce, ana sukar aikin gwamnatin APC. Jama’a sun buge da neman Jagora, kuma kamar tunbuke Sanusi II ya sa an fara yi masa wannan kallo.


Jigon adawar ya ce Sanusi II zai samu karbuwa a Arewa da Kudancin Najeriya, haka wajen ‘Yan zamani da kuma gidajen sarauta da Talakawa, da kuma goyon baya daga manyan Duniya.


Har yanzu dai sarkin bai koma kan wannan batun ba ganin har yanzu bai murmure ba balle ya ɗauki saitin abin da zai yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *