Spread the love

Ƙungiyar fataken Shanu ta Zamfara ta ƙara tabbatar da goyon bayanta ga samar da tsaron jiha


Daga  Aminu Abubakar Mayanchi Gusau

Ƙungiyar fataken shanu reshen jihar Zamfara ta tabbatar da goyon bayanta ga gwamnatin jihar kan yaƙar rashin tsaro da ke taɓa tattalin arzikin jihar Zamfara.

Shugaban ƙungiyar Alhaji Aminu Garba Gusau ya bayar da tabbacin ga manema labrai a birnin Gusau hidikwatar jiha. 

Ya ce Mambobisa suna aiki kullum domin tabbatar da duk wata Saniya da aka sato ba a sayar da ita kasuwa ba, a cewarsa in muka bar sayen shanun sata dole su daina kawo su kasuwa.

Shugaban ya ci gaba da cewa sun yi nasara a matakan da suke ɗauka na hana sayar da shanun sata, haka kuma sun kange mambobinsu ga yin kowane harmtaccen kasuwanci.


 Alhaji Aminu ya ƙara da cewar ƙarin haraji da mambobinsu suka koka da haka yau abin ya wuce don gwamnatin tarayya da ta jiha da jami’an tsaro da abin ya shafa sun shiga cikin lamarin.

Haka kuma ya ba da tabbacin cikakken goyon baya  mambobinsa ga tsare-tsare da shiraruwan gwamnati don kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *