Spread the love

Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga shugabanni a Nijeriya na kowane bangare su tashi tsaye a tabbatar da an shawo kan wannan matsalar ta annobar cutar Korona-baros da ta watsu a duniya take salwanta rayuwar mutane.

Gwamna ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake garin Asaba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara matsa kaimi musamman ta rufe filayen tashi da saukar jiragen sama a dukkan fadin Nijeriya.

Ya ce a lokacin da ake cikin halin neman agaji ba batun suka kuma hakkin kowa ne duba wani abu bayan walwalar jama’a. ‘Mu shugabanni akwai bukatar mu tashi tsaye ga wannan kalubale dake gabanmu, ina amfani da wannan damar in yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara matsa kaimi musamman wayar da kan jama’a ga wannan cutar da matakan da yakamata su dauka, akwai bukatar rufe filayen jirgin saman kasa’ a cewarsa.

A jawabin da mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya rabawa manema labarai a Sokoto ya ce gwamnan ya yabawa dan uwansa na jihar Delta kan hangen nesansa musamman gina cibiyar kula da maras lafiya da ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *