Spread the love

Tambuwal ya ƙaryata zancen da ake yaɗawa na baiwa ‘yar wasan Hausa Madam Korede muƙami a gwamnatinsa 


Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nisanta kansa kan labarun ƙarya da ake yaɗawa wai ya nada ‘yar wasan Hausa da ta fito a wasu wasan barkwanci Maryam Aliyu Obaje wadda aka fi sani da Madam Korede muƙamin babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan Sokoto kan harkokin sadarwar zamani.

A bayanin da mai baiwa gwamna shawara kar hakokin yaɗa labarai Muhammad Bello ya fitar ga manema labarai ya yi kira ga jama’a su fita batun zsncen da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta don ƙarya ne.

A cewar gwamna wanda a halin yanzu yana jihar Delta ya tabbatar bai yi irin wannan muƙamin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *