Spread the love

‘Yan sandan jihar Kaduna a jiya Laraba sun gabatar da mata biyar a gaban kotun shari’a dake magajin gari Kaduna kan zarginsu da shan tabar Marijuana ko wiwi a gaban jama’a.

‘Yan sanda sun zargi Amina Idris Bawa da Hauwa Salihu da Halima Murtala da Na’ima Lawa da Zahara Adamu kan saba doka guda biyu Shan tabar da kuma ɓata zaman lafiyar mutane.

Mai gabatar da ƙara Shu’aibu Ibrahim ya shaidawa kotu an kama wadanda ake zargi ne a 13 ga watan Maris din nan a lokacin da ‘yan sanda ke sintiri kan hanyar Kigo a Kaduna, in da aka kama matan suna shan tabar a wurin.

Alkali Muhammad Adam Shehu ya bayar da su beli ya ɗaga cigaba da shari’ar har zuwa 26 Maris a fara sauraren ƙarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *