Shugaban jam’iyar APC Kwamared Adams Oshiomhole a jiya ya shiga ofis bayan sati biyu baya zuwa Ofis din ya ce ya koyi darasi.

Shugaban shi ne ya jagorancin taron shugabannin gudanarwar jam’iyar a Abuja taron ya kwashe kusan awa biyar ana gudanar da shi a karshen zaman an fito da sanarwar janye dakatarwar da aka yi wa mataimakin shugaban jam’iyar na Arewa gaba ɗaya Sanata Lawal Shu’aibu da mataimakin shugaba na arewa maso yamma Inuwa Abdulƙadir.

Dakatarwar da aka yi wa mutanen tana cikin abin da ya ƙara kawo yamutsi a jam’iyar.

Taron zaman ya samu halartar shugabannin jm’iyar gaba ɗaya bayan Bulama da Shu’aibu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *