Spread the love

Jam’iyar APC reshen jihar Kano a jiya ta roki Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i ya kirkiri sabuwar masarauta ya baiwa tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi.

Gwamnan Kaduna ya nuna goyon bayansa ga Sanusi tun sanda aka tube shi har ya nada Chancellor da mataimakin shugaban hukumar bunkasa jiharsa, ya tafi wurinsa har ya samu ‘yanci ya tafi Lagas.

A bayanin da mataimakin shugaban jam’iyar APC Shehu Maigari ya sanyawa hannu, sun nemi gwamnan ya nada tsohon sarki jagora a sabuwar masarautar da suke son ya kirkirawa Sanusi.

Jam’iyar ta ce Gwamnan ba ya yin abun da jam’iyar za ta samu nasara yana sukar jagororinsa kan haka kuke kiransa da ya kirkiri sabuwar masarauta ya baiwa Sanusi a Kaduna sai a yi masarautar Kaduna da za ta dauko daga Rigachikun zuwa Kasuwar magani shi kenan ya ajiye gwaninsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *