Cigiya: Kwanaki 227 da ɓacewar Abubakar Idris Dadiyata

Cigiya: Kwanaki 227 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata


Daga Salisu Magaji Fandalla’fih


Matashi Abubakar Idris Dadiyata ya cika kwanaki 227 da bata tin bayan da wasu da ba’a san ko suwaye ba suka dauke matashin a gida.


Tun a ranar 1 ga watan Agustar 2019, wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba, suka je har gidan matashi dake jihar Kaduna suka dauke shi, lamarin da yayi sanadiyyar har zuwa yanzu babu labarinshi.


Hukumar DSS da aka zarga tun farkon ɗauke matashi, ta bayyana cewa bata tsare da matashin, hasalima bata tura jami’anta unguwar su Abu Dadiyata aiki a wannan dare ba.


Dadiyata, malami ne a jami’ar Katsina, ya kasance dan gwagwarmaya da Mai sharhi musamman a kafar sada zumunta Yana da Iyali ga iyaye Kwana 227 ba tareda sun ganshi ba.


Yana Matukar buƙatar addu’ar Ku, ‘Yan Uwa Allah ya bayyana shi, ya faranta ran  iyalinsa. Allah ya bayyana shi ko iyalinsa da danginsa za su samu saukin tashin hankalin da suke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *