Spread the love

 An dakatar da gudanar da Mauludin Ibrahim Inyas da za a yi Sokoto da Abuja

An dage  maulidin Shehu Ibrahim Inyas  da Za’ayi a Abuja da Sokkoto dukansu kafin wannan dakatarwa an shardanta gudanar da su a ranar Assabar mai zuwa, in da mahalartan za su fara shigo garuruwan a ranar Laraba domin yin wasu hidimomi kafin ranar gudanar da Mauludin.

Maula Sheikh R.T.A ya ce; a sanar da Yan’uwa cewan taron da suka Gayyata za a yi an daga shi duka saboda abin da yake Faruwa a Duniya na Cutar  CoronaVirus.

Saboda taron  bana  ‘yan Nigeria ba ne akwai kasashe da dama ne suke zuwa, to yanzu har takai ga ba’a zuwa Jam’in Sallah, ba’a zuwa Ziyara Raudar Shehu Tijjani R.T.A a Morocco da sauran wurare.

Saboda haka ake sanarda Yan’uwa cewar a yi hakuri sai kuma zuwa wani Lokaci za’a sanar Insha Allah.

Managarciya ta samu sanarwar dakatarwar ne daga turakar Rahama Abdulmajid ta facebook in da ta kawo sanarwar guda biyu ta farko daga bakin sheikh Dahiru Bauchi ta biyu daga fadar jikan Shaikh Ibrahim Inyas.

Wannan sanarwar ce ke nuna masu sana’ar da suka kawo kayansu na sayarwa suke shirin baja hajojinsu a kasuwa kenan za su sake nunke kayan su kulle jikarsu su koma sai wani lokacin na gaba da za a sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *