Spread the love

‘Yan sanda sun sanya dokar hana Acaɓa da sayar da Shayi a Sokoto


Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto sun sanya dokar hana Achaɓa da babur ko adaidaita wanda ake kira Agwagwa da buje da  sayar da shayi a teburin mai shayi daga bakin 11 na dare zuwa 6 na safe.


A yunkurin da rundunar ke yi na shawo kan matsalar fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran aiyukkan ɓatagari ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim S. Ka’oje ya ba da umarnin. 

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Muhammad Abubakar Sadik ya fitar amadadin kwamishina ya ce an sanyan dokar hana kabukabu daga 11 dare zuwa 6 na safe ban da wadan da ke da uzuri.

Ya ce haka ma mai shayi zai rufe daga 11 dare shi ma zuwa 6 safe.

Ya yi kira fa mutanen su zama masu biyar doka a cikinlamurransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *