Spread the love

Kan shirye-shirye taron majalisar zartarwar jam’iyar APC a gobe daya daga cikin jagororin jam’iyar Tinubu ya sanar da matsayarsa ta goyon bayan shugaban jam’iyar Adams Oshiomhole ya ci gaba da jagoranci, shi ne kashin bayan wanda ya kawo shugaban na yanzu ya yi tsaye sai da ya kawar da tsohon shugaban Onyegu da yake da goyon bayan wasu gwamnoni a jam’iyar.

Burin da Tinubu yake da shi na zama dan takarar jam’iyar APC a 2023 yana da bukatar shiri mai kyau don cika burinsa, ana ganin da ya rasa shugaban jam’iya burinsa kamar ya mutu ne.

Bayanan da ke fitowa matukar shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sa bakinsa ba a gobe da zaran an fito daga taron wani ake magana ba Oshiomhole ba.

Wata majiyar ta ce jam’iyar ta rabe gida biyu da masu son Oshiomholen ya ci gaba da masu ganin ya tsaya haka nan, shugaban kasa shi ne koli ga jagorancin jam’iya yana da rawar da zai taka jam’iyar ta zama abu guda ta dunke wuri daya. Akwai bukatar kamar yadda aka san matsayar Tinubu a san matsayar Buhari shi ma.

Rigimar ta sanin matsayar Oshiomhole ta shiga cikin kungiyar gwamnonin jam’iya da ciyamomin jam’iya na jihohi da majalisar gudanarwar jam’iyar.

Gwamnonin jam’iyar ma sun dare gida biyu Gwamnan 10 ke goyon bayan cigaban Oshiomhole ya yin da sauran basa goyon baya, amma a dukkan gwamnonin gwamnan biyu ne suka fitar da matsayarsu gaban jama’a gwamnan Edo ya nuna baya goyon bayan Oshiomhole yayin da gwamnan Imo ya nuna karara goyon bayansa kan shugaban APC da kotu ta dakatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *