Jam’iyar PDP a jihar Sokoto za ta yi zaben sabbin shugabanninta a gobe Litinin in da zata fara da zaben shugabannin mazabu a dukan fadin kananan hukumomi 23 dake cikin jihar.

PDP a jihar ta yi jinkirin soma zaben bisa wasu dalilai da ba a sanarwa manema labarai ba, in da wasu mutane ke danganta jinkirin ya faru ne kan yanda ake son a tsara lamarin zaben domin ka da ya bar baya da kura.

A yau Lahadi mai girma gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi taron masu ruwa da tsaki na jam’iyarsu domin tun karar zaben a gobe in da ya yi kira da a gudanar da zaben lafiya cikin lumana da baiwa ‘yan jam’iyar damarsu cikin adalci da mutuntawa.

Shugaban kwamitin sanya ido ga zaben wanda uwar jam’iyar ta turo Mista Ozorvati ya yaba da tsarin da jam’iayar take kan shi a jihar da irin jagorancin da gwamna ke yi na hada kan ‘ya’yan jam’iyar wuri daya. Ya yi fatan kammala zaben lafiya cikin lumana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *