Spread the love

Nijeriya na kusa ga kara shiga cikin matsin tattalin arziki

Daga Muhammad Muhammad

A shekarar 2014 watan Yuni da kasuwar danyen man fetur ta sauka daga farashin ganga daya a dalar Amerika 114, ta koma kan dala 30, ba sai an fadi ba duk dan kasa ya san tattalin arziki yana cikin matsananciyar matsala kuma haka aka shiga matsin a lokacin.

A 2015 gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbi mulki aka tabbatar da ana cikin matsin tattalin arziki, a 2016 abin ya kasa bunkasa haka aka yi ta koke da neman dubarun yanda za a yi, a 2017 abin ya dan canja kan wasu matakai da aka dauka, shekara uku baya Nijeriya na ta fadin Kalmar matsin tattalin arziki, har dai gwamnatin kasa ta fitoo ta ce yanzu an fita cikin matsin duk da wannan ikirari da hukumomi suka yi talaka a Nijeriya bai ga wani sauyi ba, kai kara sanya shi ma aka yi cikin rashin tabbas da kuncin talauci, tau yanzu ga kuma wani matsin tattalin arzikin na fuskantar kasar.

Masana sun nuna da wuya Nijeriya ke kaucewa shiga halin matsin tattalin arziki a yanzu in ka yi la’akari yawan bashin da take fama da shi ga kuma kasuwar man fetur da Gas da ta dogara da ita ta fadi warwas a duniya akwai matukar wahala kasar Nijeriya ta ki fadawa cikin matsin tattalin arziki.

Sun ce duk kasar da ke da arzikin man fetur take sayar da shi saman ga dala 30, yanzu tana cikin matsala domin farashin ya sauka ga lamurran tafiyar da kasa nan birjik harkar tsaro da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *