Spread the love

Magoya bayan jaruman finafinnan Hausa Adam A. Zango da Ali Nuhu sun nuna farincikinsu yanda ya taya abokin sana’arsa murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau Lahadi.

Da safen yau ne Zango ya rubuta a turakarsa ta Facebook “Happy Birthday Boss” in da ya daura hoton Ali a kasan rubutun. Bayan ya daura wannan ne fa a masoyansu suka rika shigo da yin nasu kalamai na nuna farincikinsu ga wannan shirin na yin silhu a tsakaninsu, a lokacin wannan rubutun an samu sama da mutum 200 sun yi magana kan lamarin.

Ranar haihuwar za ta zama silar sake rufe barakar da ta kunno kai a tsakaninsu a can baya, su sake komawa abu daya a matsayin yaro da ubangida kamar yadda Zango ya kira Ali mai gida.

Hatsaniya a tsakanin jarumman na Kannywood ba wata abu ce sabuwa ba an yi ta ganinta ana kuma silhuntawa komi ya wuce su cigaba da sha’aninsu a tare, tun bayan wani silhu da aka yi masu gabanin su hadu a kotu ba ka sake ganinsu a tare ba, kowa ya ja nasa daga, sai yanzu ne Adamun ya taya murna ga Ali abin da ake kallon yunkurin yafe juna da cigaba da tafiya tare kamar yadda aka soma tun farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *