Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pant

Ministan shari’r kasar Abubakar Malami, SAN, ya ce ba shi da hannu wajan sauke rawanin tsohon sarkin Kano.

Malami ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi ta hannun Dakta Umar Gwandu kamar Yadda Daily Nigeria ta ruwaito.

Ministan ya sanar da cewa maganar na gaban kotu don haka ba zai yi tsokacin komai a kai ba. Antoni janar din kasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce bashi da hadi da sauke rawanin tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da kuma mayar da shi zuwa jihar Nasarawa.

Malami ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi ta hannu Dakta Umar Gwandu, mataimaki na musamman gare shi ta fannin yada labarai.

“Maganar sauke rawanin basaraken an mika ta gaban shari’a kuma ana duba ta. Don haka ba zanyi tsokaci a kan maganar da ke gaban kotu ba.”

Sanusi ya yi ikirarin cewa Antoni janar din jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar din kasa ne suka ba hukumar jami’an tsaro ta fararen kaya da ‘yan sanda umarnin tsaresa.

Idan baku manta ba kwanakin baya mun ruwaito cewa, tubabben sarkin Kano din a ranar Alhamis ya maka sifeta janar din ‘yan sanda Najeriya, Mohammed Adamu, Darakta janar din DSS, Yusuf Bichi, kwamishinan shari’ar jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan zarginsu da tsaresa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *