Ƙudurin masu son tsayawa takara a 2023 yana lalata jam’iyyar APC kamar cutar Coronavirus – Bola Tinubu

Ƙudurin masu son tsayawa takara a 2023 yana lalata jam’iyyar APC kamar cutar Coronavirus.


Ɗaya daga cikin  jigo a jam’iyyar APC mai mulkin kasa kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu,  yace ƙudurin masu son tsaywa takara a shekarar 2023 yana lalata jam’iyyar APC tamkar cutar numfashi ta Coronavirus da take yin lahani a duniya.


“Suna harhaɗa abubuwan da babu wani mai hankali da zai haɗa su domin neman cika burin kansu. 


Alamomin rashin biyayyar da suke yi wa jam’iyyar APC yana nuna yiwuwar cewar za’a san matsayar harkokin siyasar shekarar 2023 tun kafin ficewar shekarar 2020″ Inji Tinubu.


Bai kamata su riƙa ƙoƙarin kawar da hankalin Shugaban ƙasa ga aikin ƙasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *