Spread the love

Daga Muhammd Muhammad

Daya daga cikin Masu shirya finafinnan Hausa wanda yana cikin masu kudin a masana’antar shirya finanan Hausa, ya shirya finafinnai masu yawa da aka samu nasara samun miliyoyin kudi a cikinsu, ya sake kafa wani taarihi na shirya wani fim da ya hada mutanen kudu da Arewa da ya lakume makudan miliyoyin kudi har naira miliyan 35, a zantawarsa da jaridar Blueprints ya tabo abubuwa sosai a masana’antarsu.

Bashir Mai Shadda dan shekara 30 ne a rayuwarsa ya shirya zai auri daya daga cikin ‘yan wasan Hausa da yake masana’antar tare da ita.

“A halin yanzu ban yi aure ba amma ina kan hanya zan auri daya daga cikin ‘yar wasanmu a Kannywood nan ba da jimawa ba. Muna son mu aure su ne don yadda mutane ke yi mana mummunar fahimta.”

Ya ce duk wanda yake kallon finafinnansa zai fahimci akwai wata budurwa koyaushe za ka ga ganta cikin finafinnansa, tau ita ce zai aura saboda bayan sanin kanta da ta yi da girmama mutane, ta shiga zuciyarsa kuma magabantansa sun aminta ya aure ta.

Ya ce Aisha Aliyu Tsamiya tana cikin mata masu kamun kai a masana’antar Kannywood koyaushe suna alfahari da ita ba ka taba jinta cikin wani abu da bai dace ba. Wasu mata ne suka shigo cikin masana’antar Kannywood kawai don su samu kudi su ne wadan da suka bata mana sana’a, amma shirya fim sana’a ce mai kyau.

Tun da abu ne mai kyau za ka bar matarka ta ci gaba da yin fim? Ya ce za ta zama mai shiryawa dai, ‘ya’yana ma ba za su yi wasan Hausa ba. Zan kai su makaranta mai kyau su zama likitoci da lauyoyi, saboda ni karatuna a Difiloma ya tsaya, ina son in koma makaranta na mallaki takardar digiri. Muna cikin sabuwar duniya in ba ka da ilmi mai inganci da wahala ma ka iya gudanar da kasuwancinka. A cewar Mai shadda.

Burinsa na gaba bai fi ya auri masoyiyarsa ba ya koma makaranta, ya zama Furodusa na kasa da kasa. Duk da yanzu ya gina gida ya tafi Umara da Hajji da yawa, akwai canji a asusun ajiyarsa yana son kari duk da hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *