Spread the love

Jam’iyar APC a Sokoto  ta maka hukumar zaɓe kotu saboda ta ƙi aminta da ɗan takararta a zaɓe Keɓɓe.


Jam’iyar APC reshen jihar Sokoto ta maka hukumar zaɓe kotu saboda ta ƙi aminta da ɗan takararta a zaɓen ranar Assabar da za a gudanar na ɗan majalisar dokikin jiha mai waƙiltar ƙaramar hukumar Keɓɓe.

Jam’iyar ta soki hukumar zaɓe kan haɗa kai da jam’iyar PDP a Sokoto musamman halin da shugabn hukumar a jiha Sadiƙ Abubakar Musa ke yi a jihar.

Jam’iyar ta nemi hukumar zaɓe ta sauya dan takararsu a zaɓen saboda ya janye da ƙashin kansa abin da hukumar ta ce ba zai yi wu ba don ba mutuwa ya yi ba, suna canja ɗan takara ne kawai saboda mutuwa.

A hirar da aka yi da shugaban jam’iyar APC na jiha Alhaji Isa Sadiƙ Achida  ya ce a tsarin zaɓe babu wata hujjar ƙin karɓar ɗan takararsu da suka canja saboda janyewar na farko, dokar zaɓe ba ta faɗi lokacin da za a rufe karɓar dan takara a zaɓen cike gurbi ba. A cewar Achida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *