Fadar shugaban ƙasa ta ƙarya ta masu faɗin wani matashi ya kaiwa Buhari farmaki a Kebbi.


Shugaban ƙasa ya tafi jihar Kebbi ya buɗe wasar gargajiya ta kamun kifi, wannan shi ne karon farko da bukin ya gudana bayan shekara 11 kan harkokin tsaro
A lokacin da shugaban ƙasa yake duba kayan da aka ba za a wurin ana ɗaukar hoto tare da manoma sai wani matashi da ya matsu ya ga shugaba Buhari a kusa da shi, anan ne ya yi yunƙurin ya sadu da shi.
Amma jami’an tsaro sun hana har matashin ya nuna rashin jindaɗinsa da ba a bari ya gaisa da Buhari ba, amma sai ga wasu na yaɗa bidiyon da cewa wai hari aka kawowa shugaban ƙasa. 


Wannan bayanin ne mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina ya wallafa a turakarsa ya ce anason juya abin ga abin da bai dace ba.

Managarciya ta samu labarin jami’an tsaro sun harbi matashin ƙafa, gaisuwar da ya tafi yi ta jawo masa ciwo kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *