Spread the love

Babbar Kotun tarayya ta bayar da Umarnin sakin tsohon sarkin Kano da gaggawa

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin a gaggauta sakin tuɓaɓɓen sarkin KanoSanusi Lamiɗo Sanusi da gaggawa a in da ake tsare da shi a garin Awe.

Alƙali Anwuli Chikere ne ya bayar da umarnin bayan ya saurari ƙorafin lauyan Sanusi babban lauya Lateef Fagbemi (SAN) wanda ya gabatar da ƙorafin kan lamarin.

Ana ƙarar shugaban ‘yan sanda na Nijeriya dana hukumar tsaro ta farin kaya da Ministan Shari’a kan sun tsare Sanusin ba bisa ƙa’idar doka ba.

Yanzu abin jira a gani za su bi umarnin kotu su sake shi domin ya tafi ya zauna in da yake so ba tare da kowace tsangwama ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *