Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da dama ga majalisar zartarwar jam’iyar APC ta ƙasa su shirya taron gaggawa da aka bukaci gudanarwa aranar Talata mai zuwa, kamar yadda wata majiya ta sanarwa jaridar daily trust.

Majiyar ta ce tun da har Buhari ya aminta a kira taro zai halarta.

Ɓangaren shugaban jam’iya da aka dakatar Admas Oshiomhole suna ƙoƙarin samun umarni daga kotu na hana zaman taron na gaggawa.

Sanarwar zaman mitin din da muƙaddashin sakataren jam’iya na ƙasa Victor Giadom ya fitar ta haifar da rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin gudanarwar jam’iyar, in da aka samu masu goyon baya da akasin haka.

Jam’iyar ba ta da shugaban jam’iya tun lokacin da Babbar kotu a Abuja ta dakatar da shi duk da kotun tarayya dake Kano ta ba da umarnin ya cigaba da zama kan kujerarsa ba abin da ya canja.

Wata majiyar ta ce duk abin da ɓangaren Adams za su yi na hana zaman suna kan yi don suna tsoron zaman akwai yiwuwar tsige Adams a wurin.

A hidikwatar jam’iyar an yi rabon abin makalawa Tags duk wanda ba ya da shi ba a aminta ya shiga mitin ɗin ba. Oshiomhole da mutanen ɓangarensa ba a ba su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *