Spread the love

Kusan Almajirrai miliyan biyu ne ke yawo suna gararamba a saman titunan jihar Zamfara Daraktan kasafi a jihar Alhaji Hamza Salisu ne ya faɗi hakan a ranar Laraba a birnin Gusau a wurin tattaunawa kan shirin ƙarfafa yara da ƙarfafasu a cikin al’umma wanda save the children ta ƙasa da ƙasa ta shirya.

Ya ce ƙididigar da ke tare da mu kusan almajirrai miliyan biyu ake da su a dukkan jihar dole mu kalli wannan na ɗaya daga cikin tarnaƙin jihar nan ga samu cigaba a lokutta masu zuwa.

Ya ce gwamnati na da ƙarfin da take kawo wasu tsarukka da za ta yi wa lamarin almajirci sake fasalin fuska, amma ɗaiɗaikun mutane da gungun jama’a da ƙungiyoyi suna da rawar da za su taka don fadakar da mutane ga lamarin almajirci.

A jawabinsa Daraktan shari’a a majalisar dokokin jihar Zamfara Nasiru Jangebe ya ɗaura laifi ga wasu malaman addini dake yi wa ayoyin ƙur’ani hawan keken ƙwato don su kare bara a saman titi wadda take al’ada ce a cikin al’umma.

Kodineta na UNICEF a ɓangaren ilmi Mustafa Shehu ya ce abubuwan da ke ƙara kawo matsalolin tsaro cikin al’umma ƙaruwar yaran da ba su zuwa makaranta da masu bara kan titi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *