Spread the love

‘Yan majalisar jihar Zamfara sun mayar da zaman majalisa a sabuwar makarantar Furamare da aka gina, biyo bayan gyaran da ake yi masu a zauren majalisar dokokin jiha.

Malam Mustapha Jafaru Kaura jami’in hulda da jama’a na majalisar ya fitar da bayanin a Gusau.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayar da kwangilar sake gina zauren majalisa.

Ya ce biyo bayan sake gina zauren gaba daya da gwamnatin jiha ta bayar a yanzu sun koma sabon wuri na wuccingadi, a sabuwar makarantar da aka kammala ginawa dake bayan hidikwatar hukumar bayar da ilmin furamari bai daya a Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *