Spread the love

Matasa a Sokoto sun yabawa Sanata Wamakko kan mukamin da ya baiwa daya daga cikin jajirtattun matasa a jihar

Muhammad Muhammad

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya nada matashi Nasiru Aminu Bazza mukamin mataimaki na musamman kan harkoki na musamman, mukamin da aka baiyana wanda ya dace ya zo kan lokaci ganin yanda Sanatan aikinsa da kokarinsa da muradinsa kan jiharsa ke bukatar samun jajirtattun matasa a kusa da shi domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

A takardar kama aiki da Daraktan mulki na Satan Alhaji Mustapha Abubakar Alkali ya sanyawa hannu ta ba da zabi ga wanda aka baiwa mukamin na karba ko akasin haka a cikin sati biyu da ba shi mukamin.

 Bayan fitar takardar ta mukamin a kafofin sada zumunta matasa a jihar Sokoto kamar Sama’ila Sani Yabo da Mubrak Abubakar Balle da wasu matasan sun yi fatan alheri ga sabon mukamin bayan taya murna da suka yi.

Kabiru Suleiman wani matashi ne a jihar ya ce mukamin abin alfaharinsu ne su matasa domin duk wanda ya san wannan matashin Nasiru Bazza ya san shi da jajircewa kan samarwa matasa makoma mai kyau, in har yana samun irin wannan cigaban matasa ma sanyawa a ransu za su samu makoma mai kyau wadda za su taimaki al’umma da yankinsu.

Usman Shehu dan shekara 29 ya ce mukamin da sanata ya baiwa daya daga cikinmu da muke koyi da su ya kara nuna mana Sanata ba zai taba mantawa da mu ba muna cikin ransa ya kuma yarda mu ne kashin bayan cigaban al’umma, saura da mi kar ya bamu kunya ya yi aiki tukuru domin kawo cigaban jiharmu da al’ummarmu, matasa na fuskantar kalubale da yawa ya dubi abin da zai fara sanya wa gaba don kawo sauyi a mukamin da aka ba shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *