Spread the love

Buhari ya ce ba shi da hannu ga cire tsohon Sarkin Kano


Muhammad Muhammad


Shugaban ƙasa  Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da hannu a tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Umar Abdullahi Ganduje ta yi.


Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya wallafa haka a shafinsa na facebook in da ya bayyana cewa duk maganganun da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce.


Ya bayyana cewa shugaban ƙasar bai taɓa katsalandan a cikin harkokin wata jiha a ƙasar ba sai dai idan hakan ya shafi tsaron kasar baki daya.


Idan ba a manta ba dai, a hirar da aka yi da Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa Buhari na da hannu a tsige tsohon Sarkin shi ne fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga kalaman Sanatan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *