Spread the love

DAN MAJALISA DAGA JAHAR SOKOTO ZAI GABATARDA KUDURIN GYARA HARKOKIN ALMAJIRANCI A NAGERIYA

Daga, Jamilu Sani Rarah da Sani sabo

A gobe Alhamis ne Hon. Balarabe Shehu Kakale Shuni Mai wakiltar Kananan hukumomin Dange Shuni, Tureta da bodinga zai gabatarda wata muhawara a zauren majalisa tarayya dake Abuja

Da yammacin yau, tawagar ta Hon.Balarabe Shehu Kakale Shuni suka bar filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sarkin Musulmi Abubakar Na III dake Sakkwato domin karba goron gayyata na su shaidi zaman majalisar wakilai ta Kasa a gobe alhamis domin gabatar da muhawara akan inganta tsangayar Almajirai da Almajirci a Najeriya domin dogaro da Kai da samar da tsaro a Najeriya.

Wannan ne karon farko a tarihin siyasar wannan mazaba dake a jihar SAKKWATO, da wani Danmajalisa ya dauki nauyin gayyato al’ummar mazabar sa, da wasu masana tareda masu ruwa da tsaki a kan sha’anin ALMAJIRCI domin su saurari muhawara da za’a gabatar a zauren Majalisar Wakilai ta Kasa.A cikin tawagar akwai masu baiwa Gwamnan jihar SAKKWATO shawara Alhaji Ibrahim Muhammad Ardo Shuni,Alhaji Yusuf Dingyadi, Zayyanu Marafa Shuni,Sakataren Mazabar Danmajalisar wakilai ta Bodinga,Dange Shuni da Tureta Musa Sabo Shuni,Hajiya Ubaida Bello Muhammad, Amira Amina Sakaba.Akwai Limamai daga Masallatan Jumu’a dake garin Tureta,Bodinga Dange da Shuni.

Sai Shugabannin Makarantun Allo/Zaure da kuma wasu daga cikin Almajirai dake BODINGA, DANGE SHUNI da TURETA wadanda Danmajalisar wakilai Balarabe Shehu Kakale zai gabatar da su a matsayin gwaji ga irin tsarin Almajirai da yake so majalisar ta aminta da shi a matsayin tsarin Ilimin Almajirci domin samar da Yara masu Hazaka, Ilimin lissafi,Kimiyya,koyon sana’o’i domin su zama masu dogaro da Kai domin samar da tsaro da cigaban kasar mu Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *