Spread the love

 
Daga Comr Abba Sani Pantami


Mai martaba tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya yi alƙawarin ɗaukar matakin doka a kan gwamnatin jihar Kano bisa abin da ya bayyana na tsare shi da gwamnatin ta yi da tsare-tsaren da aka bi na tsige shi ba bisa ka’ida ba a ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.


A ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sauke mai Martaba bisa zargin karya doka da al’adun masarautar jihar.  

Don haka, aka tura sarkin zuwa jihar Nasarawa inda ake tsammanin zai karasa rayuwarsa.


Ko da yake, kungiyar lauya ta Mista Sanusi, karkashin jagorancin Abubakar Mahmoud, SAN, a wata gana da manema labarai ranar Talata, ta ce sun samu umarnin ne daga tsohon sarkin da aka tsige don ƙalubalantar tsare shi da kuma korarsa a gaban kotu kotu.


Mista Mahmoud ya yi korafin cewa, a ganinsu, tsigewar ba ta bisa doka kuma ba a bi  doka wajen aiwatarwar ba, yana mai kira ga gwamnati da ta sake duba hukuncin cikin awanni 24 ko kuma su dauki matakin doka.


 “Bisa umarnin da muka samu daga Sarkin ta bakin Shugaban Ma’aikata, an umurce mu da mu ɗauki matakin doka don ƙalubalantar gaskiyar tsarewar da korar Sarkin.


 “Muna da yakinin cewa wannan mataki doka da oda ce. Sashe na 35 na kundin tsarin mulkinmu ya ba da tabbaci ga kowane ɗan ƙasa yana da ‘yancin walwala na shi.


Wannan bayani na nuna cewa za a yi shari’a tsakanin gwamnatin Kano da tsohon sarkin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *