Spread the love

Tsohon shugaban Najeriya, Janaral Abdussalam Abubakar, ya bayyana rashin jin dadin shi bisa ga tsige Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi ll daga mulkin Kano.

A  jiya Litinin ne gwamnatin Kano karkashin Gwamna  Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarkin  tare da maye gurbin shi da Alhaji Aminu Ado Bayero cikin awowi kadan.

 Abdussalam ya bayyana shakkunsa a kan rashin saka bakin shugaba Muhammadu Buhari a cikin rikicin, inda ya bayyana cewar in har shugaban ya sanya baki, to lallai akwai mamakin jin tsigewar Sarkin, yana ganin da wuya Buhari ya sa baki ga maganar Gwamnan ya yi kememe ya zartar da wannan Karen aikin da bai yi dadi ga al’ummar Arewa ba.

 Tsohon shugaban ya yi hira da sashen Hausa na Muryar Amurka, ya bayyana tsige Sarkin a matsayin abin bakin ciki.

“Abinda zance Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, wannan labari ne mummuna, muna fata Allah Ya kauda fitina a Kano bisa wannan abin da aka yi.”

“Allah ya gani, munyi iyakacin kokarinmu, mu zauna da gwamna da Sarki, mun kuma basu shawarwarin abin da mu muka ga yakamata a yi, bayan mun gama aikin mun ga alamar an samu nasara”

 Ko shugaba Buhari ya sanya baki acikin rikicin da yake tsakaninsu? Ya ce  “To a halin yanzu bazan iya cewa ko shugaba Buhari ya sa baki a wannan magana ko bai sa ba domin bana Najeriya, amma kafin in taso lokacin da muka mika masa bayanan da muka tattara, mun tattauna da shi kuma ya nuna mana zai sa baki don a samu masalaha, to bayanin ko ya samu yin magana, ban sani ba.” a cewarsa.

Tsohon shugaban ya sake amsa tambayar kan cewar ko rashin sanya bakin shugaba Buhari ne ya kai ga tsige Sarki? Ya ce“Ban sani ba ko ya sa baki ko bai sa ba, amma da alama ya sa baki din tun da ya karbi rahoton bincikenmu, da alama ya sa baki amma bazan iya tabbatarwa ba.”

“Kuma in ya sa baki, zanyi mamaki bayan yasa baki mu kai inda wannan abu ya faru, amma kasan komai sa baki da shawarar wani abin da Allah ya kaddara, babu mai canza shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *