Spread the love


Shugaban tashohin jiragen ruwa na Nijeriya, Hajiya Hadiza Bala Usman ta ƙaryata jita-jitar da ake yi cewa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i saurayin ta ne, wanda hakan ya sa aka ba ta muƙamin da take kai a yanzu.


Hajiya Hadiza, wadda ta riƙe mukamin shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna daga 2015 zuwa 2016, ta bayyana hakan ne a jiya Litinin a wani shiri na gidan talabijin din TVC da aka gudanar game da bikin ranar mata ta duniya.

in da ta kara da cewa gwamna Elrufai tamkar ubangida yake a gare ta.

Ta tsaya kai da fata Cewa ita ba budurwarsa ce ba, sai dai shi ubangidanta ne a siyasa kuma ta yi aiki a ƙarƙashinsa.

Managarciya na ganin irin waɗan nan kalamai ba su dace a riƙa shigo da su a tsakanin shigabannin al’ummma ba don suna rage kimar jagoranci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *