Spread the love

Tun bayan bayyana sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a yanzu hankula sun karkata zuwa wanda zai zama sabon sarkin Kano.


A doka dai zuri’ar gidan Dabo ne kawai za su iya sarautar Kano.

To sai dai zuri’ar tana da yawa kuma ta kasu gida-gida.

Kawo yanzu dai gwamnati ta bayyana nada sabon sarki in da hankula sun ka fi karkata ne zuwa gidajen Sarki gidan Ado Bayero, tsohon Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero (Gidan Ado Bayero), Aminu Ado Bayaro ne sabon sarkin Kano.

Mutane da dama musamman na kusa da gwamnati sun jima suna daukar Aminu Ado Bayero a matsayin wanda za a bai wa sarautar Kano da zarar an sauke Sarki Sanusi.

Tun shekarar 2017 aka fara takaddama tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi. Aminu Ado yana da farin jini a wajen mutanen Kano, don haka gwamnatin za ta iya nada shi don ya gaji mahaifinsa Ado Bayero, wanda har yanzu jama’ar Kano suke mutuntawa.

Aminu Ado yana da matukar tasiri cikin ‘ya’yan Ado Bayero saboda kusancinsa da mahaifinsu a lokacin da ya ke raye.
Kuma mutane da dama na ganin ya cancanta ya zama sarkin Kano saboda halayyarsa irin ta sarakuna ce.

Wasu na ganin hakan zai iya haifar da gushewar martabar sarauta a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *