Spread the love

Gwamnonin jam’iyar APC mai mulki a Nijeriya sun rabu gida uku kan ra’ayin shugabancin shugaban jam’iyarsu Adams Oshiomhole wasu daga cikin su na ganin shugaban ya tafi kawai yayin da wasu ke ganin ya cigaba, sai na uku da suka tsaya tsakiya in ya tafin daidai in ma an barshin dai ya yi.

Gamnonin jihohi da ke son a bar Oshiomhole ya ci gada jagoranci su 9 ne Aminu Bello Masari na Katsina da Abdullahi Ganduje na Kano da Babagana Umara Zulum na Borno da Hope Ozodimma na Imo da Gboyega Oyetola na Osun da Dapo Obiodun na Ogun da Babajide Sanwo Olu na Lagas da Mai Mala Buni na Yobe da kuma Yahaya Bello na Kogi.

Gwamnonin da suka hada kai da fata lalle sai ya tafi sun gaji da jagorancinsa su ne su 7 Kayode Fayemi na Ekiti da Godwin Obaseki na Edo da Oluwarotimi Akeredolu na Ondo da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da Simon Bako Lalong na Filato da Abubakar Atiku Bagudu na Kebbi da Muhammad Badaru na Jigawa.

Gwamnonin da suka yi tsaye saman katanga suka ki shiga ko’ina su ne 4 Abubakar Sani Bello na Neja da Abdullahi Sule na Nasarawa da AbdulRahaman AbdulRazak na Kwara da kuma Inuwa Yahaya na Gombe.

Wasu tsoffin gwamnoni da ba su goyon bayan Adams sun hada da: Ibinkule Amosun da Rochas Okorocha da Abdul’aziz Yari da Rotimi Amaechi.

Wannan ba karamar rigima ce ke gaban jam’iyar ba wanda sasantata sai an yi gwarzon aiki ganin yanda gwamnonin suka ja daga kusan gwamnoni masu wa’adi na biyu sun ja gefe daya sabbi masu wa’adi na farko sun ja gefe kan jagorancin jam’iyar.

Rigimar ganin sai an sauke shugaban jam’iyar nada nasaba da zaben 2023 dake tafe gwamnonin nason su karbi jam’iya a hannun shugabanta na yanzu domin su taka rawarsu yanda suke so ba tare da katsalandan ba, irin na shugaban na yanzu wanda ya yi masu a zabukan fitar da gwani na jam’iyar a 2019, kan haka yanzun ba su amince su bar shi ya cigaba ba domin rashin tabbas ko zai barsu su yi doki doran da suke so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *