Spread the love

Jaruma a masana’atar shirya finafinnan Hausa Bilkisu Abdullahi wadda aka fi sani da Balkisu Shema kyakkyawa ce daga ƙabilar fulani a zantawarta da jaridar Blueprints ta nuna gara ta bar harkar fim da producer ko daraktan fim ya santa kafin ya saka ta fim.

“Ina jin mutane na sukata wai ina ji da kaina, gaskiyar magana shi ne ba zan taɓa bayar da kaina ko nawa ba. Za ka ga wasu matan a Kannywood don su samu ɗaukaka suna iya yin komai a sanya su taka rawa a babban fim, ni ba haka nake ba kuma ba zan taɓa zama haka ba, da in kwanta da wani mai shirya fim ko daraktan fim don kawai a sanya ni fim da in yi haka gara na bar masana’antar. Mutuncina shi ne abin bugun gabana zan riƙe shi har gidan aurena” a cewar Balkisu Shema.

Da ta juya kan zargin aikata baɗala da ake faɗin ta mamaye masana’antar ta ce kafin ta shigo kannywood ta ji irin waɗan nan zarge-zarge da ake yi wa Furodososhi da daraktoci, amma da ta shiga masana’antar ta hannun wani ɗan uwanta da ya haɗa ta da Baba ƙarami har ya sa ta cikin fim da ta fara yi Aikin Duhu daga nan ta fara samun gayyata daga Furodudoshi da Daraktoci, yadda mutane ke faɗin abubuwan ba haka ba ne akwai kamun kai da mutum zai yi alfahari in yana cikin masana’antar.

Ta yi farincin yadda take harkar har ta iya zama da Ali Nuhu da Adam A. Zango abin kamar a mafarki yanzu ta yi Shekara uku a masana’antar ya kai ga bata iya tafiya a hanya ba ta hadu da dubban masoyanta ba tana farinciki da Kannywood ta ɗaukaka darajarta.

Ta ce mahaifinta ɗan asalin Kano ne mahaifiyarta ‘yar yola ce ta fito daga babban gida.

Bilkisu Shema

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *