Spread the love

Gwamnoni waɗan da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyar APC sun goyi bayan dakatarwar da kotu ta yi wa shugaban jam’iyarsu na ƙada Adams Oshiomhole.

Gwamnonin sun nemi majalisar zartarwar jm’iyar ta gaggauta cike giɓin da aka samu ta sauya shigaban da wani mutum daban.

Gwamnonin ta hannun babban daraktan ƙungiyarsu Salihu Lukman a jiya(jumu’a) ya yi kira ga Oshiomhole da ya zama shugaban jam’iyarsu a watan Yuni 2018 ya yi murabus.

Ya ce abin da kawai yafi ga Adams ya koma mazaɓarsa ya gyara matsalarsa, sun dakatar da shi a mazaɓarsa 10 a ƙaramar hukumar Etsako ta yamma jihar Edo. Tun 2 ga Nueamba 2019 shugabannin gaba ɗaya suka jefa ƙuri’ar rashin gamsuwa da shi tare da dakatar da shi cikin jam’iya.

Sun buƙaci majalisar zartarwar jam’iya su cike sauran shugabannin gudanarwa da babu don su ci gaba da aiki a matsayin muƙadasai kafin a yin zaɓen shugabannin jam’iya na ƙasa.

Muƙaman da ake son a cike su ne: Shugaban jam’iya da Mataimakinsa a ɓangaren Arewa da Mataimakinsa a ɓangaren kudu da mataimakin shugaban jm’iya a Arewa ta Yamma, da sakatare na ƙasa da Odita, a taron majalisar zartarwar jam’iya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *