Spread the love

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce sama da Almajirrai dubu takwas kananan yara wanda shekarrunsu bai wuce biyar zuwa bakwai da uwayensu suka turo a jihohi daban-daban su zo Nasarawa yin bara.

 Gwamnan ya ce Gwamnatinsa za ta kare da samar musu mafita.

Ya yi maganar ne a Abuja a lokacin da ya kai wa minister aiyukkan jinkai da samar da agajin gaggawa da cigaban jama’a Hajiya Sadiya Umar Faruk ziyara.

Ya ce ‘yan asalin jiharsa da suke gudun hijira a wasu jihohi suna bukatar taimako don su dawo gida(Jiha).

Ministar a jawabinta ga gwamana ta ce mutum dubu 48 da 637 shirin tallafin kudi ga wdan da ke cikin matsi da wasu dubu 12 da 200 a shirin N-Power a jihar Nasarawa.

A bangaren ciyarwar ‘yan makarata na gwamnatin tarayya ta ce yara 170,630 daga Furamari aji daya zuwa 3 ake ciyarwa kullum a jihar ta Nasarawa, in da aka dauki ma’aikata masu dafa abincin 2,433.

Ta ce suna da ‘yan gudun hijira a jjihar da suke kula da su a bangaren ba da agajin gaggawa, tana fatan samun goyon baya ga masu ruwa da tsaki don cimma nasarar aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *