Spread the love

Sakkwatawana sa ran su amfana da gawanar Faruku Yabo da shugaban Kasar Tanzaniya a harkokin kasuwanci da saka jari

Honarabul Faruku Malami Yabo ya gana da shugaban kasar Tanzaniya kan harkokin kasuwanci da saka jari, abin da Sakkwatawa ke sa ran su amfana da wannan tattaunawar ganin yanda yake mutum mai son cigaban jihar Sokoto duk wani abu da yake yi kan dai jihar ta cigaba ne, kuma jihar nada bukatar irin wannan hobbasar ta kulla harkokin kasuwanci tsakanin al’ummar jihar da wata kasa domin ba bangaren dake samar da aikin yi ga al’umma sama da kasuwanci.

Yariman Yabo tare da wadansu ‘yan kasuwa a Nijeriya  sun amsa gayyatar  tattaunawar da shugaban kasar  John Magufuli wadda ta gudana a babban birnin Dodoma na Kasar ta Tanzaniya ta samu shaidar jakadan   Nijeriya a Kasar Alhaji  Sahabi Isah Gada da prime Minister na kasar Kassim Majaliwa da kuma sauran mukarraban Gwamnatin kasar.

Jihar Sokoto nada albarkatun kasa da harkokin kasuwanci da take bukatar huldar kasuwanci da zuba jari don bunkasa jihhar da al’ummarta, wannan huldar ba karamar nasara da alheri za ta jawo wa jama’ar jihar ba a haujin farfado da kanana da matsakaitan kasuwancin da suka durkushe a jihar domin rashin jari da abokan huldar da za a samu kasuwanci ya bunkasa jama’a su kara samun abin dogaro da kai yana ci wa jihar Sokoto tuwo a kwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *