Spread the love

Duk da tsibin bashi da hwamnatin Nijeriya ta ciwo da alƙawalin da take yi na samar da aiyukkan da za su inganta rayuwar talakawa, amma mutum miliyan 95.9 a cikin yawan mutanen ƙasar miliyan 201.62 ke cikin matsanancin talauci.

Kamar yadda ƙididdigar ta bayyana a kashi 48 na al’ummar ƙasar ke fama da talaucin.

Ƙididigar da ake bi wajen gano talaucinku abin da ke shigo ka da gamsuwarka, da abin da ka samar da abin da kake amfani da shi, haka majalisar ɗunkin duniya da bankin duniya suka aiyana.

Talauci a allon duniya yana ga wanda baya samun dalar Amerika 1.90 a yini, na tsakkiya shi ne mai samun dalar Amerika 3.20 a kullum baya cikin talauci sai na sama wanda ke samin 5.50.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *