Spread the love

A sati mai zuwa ne gwamnatin Tambuwal za ta sanar da matsayar daliban sikandaren da suka fadi jarabawar MOCK

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana jitajita ce kawai aka rika yawo da ita na cewa gwamnatin Sokoto ta yi matsaya ba za ta biya kudin jarabawar NECO ga dalibbai ‘yan asalin jihar Sokoto da suka fadi jarabawar gwaji waton MOCK da ma’aikatar kula da ilmin Furamare da Sikandare suka shirya kuma suka aiwatar.

Gwamna Tambuwal ya yi watsi da zargin a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin da ya kafa shekara daya da ta gabata, domin tantance malamai 2000 da gwamnatinsa za ta dauka, a yau juma’a.
A bayanin da mai baiwa gwamna Tambuwal shawara Muhammad Bello ya fitar ya ce gwamna ya turmuje jitajitar da ake yadawa, a cewarsa haryanzu gwamnati ba ta dauki matakin karshe ba, sai idan ta yi zama wani sati za ta dauki matakin karshe bayan ta nemi shawara ga masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Haka kuma Gwamnan ya ba da tabbacin gwamnatinsa za ta samar da cibiya da za ta rika horasda malamai da kara ba su horaswa a jiha.

Tambuwal ya jinjinawa mambobin kwamitin kan aiki mai kyau da suka yi musamman a wurin tantancewa da zabo wadan da suka dace, nan ba da jimawa ba za su zartar da hukuncin kwamitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *