Jam’iyar APC ta ƙasa a jiya Laraba ta aika takardar neman sauya ɗan takararsu a zaɓen cike gurbi da hukumar zaɓe za ta gudanar a 14 ga watan nan a ƙaramar hukumar Keɓɓe ta jihar Sokoto.

Ofishin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa ya karɓi takardar ta su mai sa hannun dakataccen shugabansu Oshiomhole da muƙaddashin sakataren jam’iyar na ƙasa Victor T. Giadom.

Takardar tana ƙunshe da bayanin cewa, suna sanar da hukumar ɗan takararsu Abubakar Bello Umar ya sanar da su ya janye takararsa.

Kan haka suke son maye madadinsa da Alhaji Hassan B. Abubakar.

Sun sanar da hukumar a bayan takardarsu akwai fom na hukumar zaɓe EC9, EC11E, EC12E, da sauransu na ɗan takara.

A ƙarshe sun ce dafatan hukumar zaɓe za ta aminta da buƙatarsu.

Yanzu abin jira a gani matakin da hukumar zaɓe za ta dauka na gaba domin wasu na ganin lokacin sauya dan takara ya wuce kan haka ya sanya wanda ya janye ya bari sai wannan marar ya yi masu tutsu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *