Spread the love

MARTANI A KAN KALAMAN SANI YARIMA KAN BATUN SAKE DUBA FASALIN SHARI’AR ZABEN JIHAR ZAMFARA WANDA KOTUN KOLI KE KANYI DA KUMA KOKARIN YARIMA NA ALAKANTA SHARI’AR JIHAR IMO DA JIHAR ZAMFARA.

A jihar Zamfara dama Najeriya baki daya, kowa yanzu ya sheda irin salon siyasar Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura na Ungulu da kan zabo, wanda hakan yana daga cikin dalilai wanda yasa Yarima yake iya kokarinsa na ƙulleƙullen siyasa harma da kokarin ganin cewar Gwamna Bello Matawalle na jam’iyar PDP ya cigaba a saman kujerar Gwamnan zamfara duk da cewar Yarima yana ikirarin cewar shi dan jam’iyar APC ne kuma har yana shirin takarar Shugaban Kasa a jam’iyar APC a zabe me zuwa na Shekarar 2023.

Yarima ya tsorata matuka daga irin jajircewar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Jagoran jam’iyar APC na jihar zamfara Abdul’aziz Yari ganin yanda ya tsaya tsarin daka har sai ya kwatowa jam’iyar APC da mutanen Zamfara hakkinsu na wadanda suka zaba a zaben da ya gabata.

Don haka Sanata Yarima ya shiga layin maganganun marasa kan gado da ‘yan jarida kowane lokaci idan aka yi zaman sauraren shari’ar jihar Zamfara don yaɗa maganganu marasa amfani.

Yarima a cikin maganganunsa na marasa kan gado ga yan jarida, ya bayyana cewar hukuncin kotun koli wanda kotun ta yi a baya ba’a iya sake canza shi, sannan Yarima ya bayyana cewar shari’ar jihar Imo kala ɗaya ce da ta jihar zamfara ganin kotu ta yi watsi da karar jihar Imo don haka rokon itama shari’ar jihar Zamfara kotu za ta yi watsi da ita, kana kuma Yarima ya nuna Abdul’aziz Yari yana kokarin yaudarar magoya bayan jam’iyar APC ne kawai wajen nuna masu cewar kotun zata iya chanza hukuncinta na baya a cikin sauraren biyar hukuncinta na farko “Judgement review” wanda take a halin yanzu kuma zata cigaba a ranar 17th ga watan Maris, 2023.

Yana dakyau ko yanzu Yarima yasan cewar Shari’ar zaben Jihar Zamfara tasha banban da ta jihar Imo, kuma basuda wata alaka ta kusa balle ta nesa. Shari’ar Jihar zamfara ta shafi lamarin zaben fidda gwani (Primary Election) ne, wanda kuma shari’ar jihar Imo ta na a bangaren lamarin kuri’u zabe wanda akayi. Hakazalika lamarin shari’ar jihar zamfara ya shafi rigimar cikin gida daya na jam’iyar daya wato APC Zamfara, shari’ar tana kan tsakanin APC ne kacal ba tsakanin APC da PDP ba kamar yanda shari’ar jihar Imo ta ke. Abin kara lura kuma a shari’ar ta jihar Zamfara shine; Jam’iyar APC na bangaren Abdul’aziz Yari suna rokon kotu ne don sake dubi akan wasu hukunce hukunce masu sharudda (Court order) wanda kotun ta aiwatar a cikin hukuncin, wanda a jihar Imo hukuncin baki daya ne ake kalubalanta.

Sannan Yarima da yake maganar cewar kotun Supreme court ba zata iya sake sauya hukuncinta ba, wannan ba abun mamaki bane don ya fito daga bakin Yarima, domin hakika Yarima ga dukkan alamu ya jahilci lamarin shari’a ta zabe da kuma sanin hukunce hukunce da dokokin kotun koli.

Tabbas kotun koli ta Supreme court tana da hurumin sauya hukuncinta, Idan ya kasance a hukunci akwai boyayyen cin hanci da rashawa, ko akwai kuskure na zayyana hukunci, ko kuma sharuddan da kotun ta bayyana a hukunci Suna da kuskure, ko kuma an yiwa hukunci karan tsaye don boye gaskiya, ko kuma a hukuncin ba’a yi amfani da dokokin kotu ba.

Don kara ilmantarda Yarima akan maganganunsa na karya da shirme, akwai doka babba a cikin dokokin kotun koli (Oder 8 Rule 16) wadda ta baiwa kotun Supreme Court damar sauraren “Judgement review” da kuma gyara kuskure na hukuncin kotun koli a kowa ce shari’a.

Don haka duk wasu maganganun shirme da Yarima yake akan maganar Shari’ar zaben Jihar Zamfara ko alakanta shari’ar Zamfara da shari’ar jihar Imo magaji ne na dan siyasa wanda ya kare tasiri a siyasa amma yana kokarin hanya mafi sauki da za’a dinga jinsa a siyasar jihar zamfara.

Abdul’aziz Yari zai cigaba da fafutuka wajen ganin cewar an yiwa al’ummar zamfara da jam’iyar APC adalci a kotun koli wanda dukkan alamu sun fara tabbatarda nasara a bangaren Yari da APC.

Ra’ayi: Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *